Wayarka tana ɗauke da sirrinka duka—banki, hotuna, da sakonni. A wannan zamanin, hackers suna ƙoƙarin kowace hanya don su sace bayanan mutane. A shafin Bloopa, muna damuwa da tsaronka. Wannan jagorar za ta nuna maka matakan da za ka bi don kare wayarka daga kowane irin hari.
1. Avoid Public Wi-Fi for Banking
Yin amfani da Wi-Fi na fili (kamar na wuraren taro ko filin jirgi) yana da haɗari. Hackers za su iya sa ido su ga duk abin da kake yi. Idan dole ne ka yi amfani da shi, tabbatar kana amfani da VPN don ɓoye bayananka.
2. Turn Off Unnecessary Permissions
Wasu apps ɗin suna neman izinin da ba su buƙata. Me ya sa app na Calculator zai buƙaci ganin inda kake (Location) ko hotunanka? Ka shiga Settings na wayarka, ka duba App Permissions, sannan ka kashe duk abin da ba shi da amfani.
3. Use Two-Factor Authentication (2FA)
Wannan shi ne babban garkuwa. Ko da hacker ya san password ɗinka, ba zai iya shiga ba sai ya samu wannan lambar ta musamman da ake turo maka a waya. Tabbatar ka kunna 2FA a WhatsApp, Facebook, da Gmail dinka.
4. Update Your Software Regularly
Kamfanonin waya suna turo updates ne don toshe ramukan da hackers suke bi su shigo. Duk lokacin da kaga wayarka ta kawo update, kada ka yi jinkiri, yi sauri ka saukar da shi don ƙarfafa tsaron wayar.